fbpx
Friday, May 14
Shadow

Gwamna El-Rufai ya soke maganar Dan Asalin Jiha, inda ya kawo katin shaidar zama a Jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya soke maganar ace mutum dan Asalin jihar Kadunane.

 

Ya kawo katin zama a jihar Kaduna wanda yace duk wani dake zaune a jihar zai iya yinsa kuma ya amfana da duk wani abu da gwamnatin jihar ke samarwa.

 

Ya bayyana hakane a wajan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin hukumar yin rijistar zama a jihar Kaduna da kuma bankin UBA.

 

Yace za’a samar da kati wanda mutum zai iya amfani dashi a matsayin ATM ya gudanar da kasuwancinsa sannan kuma nan gaba kadan zasu mayar dashi ya zama dole a wajan amfana da abubuwan da gwamnati ke samarwa kamar su kiwon lafiya, Ilimi da sauransu.

 

Yace zasu kalli wanda ke zaune a Kadunane a matsayin da Kundin tsarin mulki ya basu na ‘yancin zama a ko ina da kuma taimakawa ci gaban Tattalin Arzikin jihar amma ba maganar dan Asalin jiha ba.

’This government has recognised citizenship as what the Nigerian constitution advocates rather than ‘indigenship’ and ‘settlership.’ We believe that the dichotomy between indigenes and settlers has brought untold problems to the country and has slowed down the unity of our great nation,” he said.

The governor further argued that Kaduna state is ‘’concerned about citizens of Nigeria that are registered as residents, that pay tax and contribute to the economic wellbeing of our state.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *