fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Gwamna Ganduje ya amince da fidda Naira miliyan N160 domin gina ofishin yan sanda, da bariki a garin kan iyakar jihar Kano

Bayan wasu rahotanni na baya-bayan nan na shigar wasu mutane da ake zargi daga Katsina, Zamfara da sauran yankuna da suka yi kaurin suna wajen yin fashi da makami ga al’ummomin da ke kan iyaka jihar Kano, Gwamnatin Jihar Kano ta amince da gina wani barikin ‘yan sanda wanda ya kai kimanin Naira miliyan 160, a tashar a garin Getso, da ke karamar hukumar Gwarzo ta jihar.

Kwamishinan Muhalli na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim Getso, ya sanar da haka a lokacin bikin aza harsashin aikin, inda ya bayyana cewa aikin zai hada da ofishin ‘yan sanda, gidaje na manya da kananan ma’aikata da masallaci ga jami’an ‘yan sanda. .

Ya kuma ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da gina wasu ayyukan ci gaba a yankin, kamar asibiti, fadada kasuwar shanu ta Getso da mayanka ta zamani wacce za ta samar da damar aiki ga matasa masu hadin gwiwa a yankin, ta yadda za a kauce musu daga shiga cikin wasu abubuwan da basu da kyau.

Dakta Getso ya ci gaba da yin kira ga jama’ar yankin da su ba da hadin kai ga dan kwangilar, yana mai ba su tabbacin cewa gwamnati za ta biya su diyya, musamman wajen sauya matsugunin motar.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo ya ba da rahoton ganin ayyukan wasu mutane wanda ba yan yankin ba,wadanda ya ke zargin yan bindiga ne da suka fito daga jihohin Katsina da Zamfara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *