Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da gudummawar Naira miliyan 3 ga Malam Abdulrahaman Ibrahim Wailari domin rage masa radadi da asarar da ya yi a wani bala’in gobara da ya mamaye gidansa kwanan nan.
Wailari, mazaunin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, ya rasa iyalansa bakwai a sanadiyar wannan gobara.
An sanar da bayar da gudummawar ne yayin bikin kaddamar da rabon kayayyakin tallafin ga mutane 1500 a jihar.