fbpx
Monday, May 10
Shadow

Gwamna Makinde ya yi watsi da ikirarin Tinubu na cewa APC za ta ci gaba da mulki gaba da 2023

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi watsi da ikirarin da Jagoran APC na kasa, Bola Tinubu ya yi cewa jam’iyya mai mulki za ta ci gaba da mulki sama da 2023.

A makon da ya gabata ne Tinubu ya kai wa Shugaba Buhari ziyara a Abuja. A yayin ganawa da manema labarai na gidan gwamnatin, jigon na APC ya ce ‘yan Najeriya suna matukar kaunar APC har za su sa jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa a ofis bayan shekarar 2023.

Gwamna Makinde ya bayyana matsayin Tinubu a matsayin karya. A cewarsa, ‘yan Najeriya sun gaji da duk irin rashin kyakkyawan shugabanci na jam’iyya mai mulki.

Yace; Na karanta a jaridar cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, ya ce APC za ta ci gaba da mulki sama da 2023, wannan karya ce babba.

Yan Najeriya sun gaji da duk irin barnar da APC ke yi a matakin kasa. Shin rashin tsaro ne? Shin durkushewar tattalin arziki ne?

Mu a jam’iyyar PDP, tun daga Kudu maso Yamma, a shirye muke don samar da shugabanci ga kasarmu. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *