fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Gwamna Ortom ya mayar da martani kan kisan Olajide Sowore

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi Allah wadai da kisan Olajide Sowore, kanin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore da wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne.

Da yake mayar da martani, Gwamna Ortom a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai, Terver Akase, ya ce mummunan kisan da aka yi wa Olajide yana kara nuna yanayin tabarbarewar tsaro a duk fadin kasa nan.

Gwamnan ya bayyana cewa yana fatan hukumomin tsaro za su kamo wadanda ke da alhakin kisan matashin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a yayin da take zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, ta ce suna kan bincike don kama wadanda suka kashe mamacin.

Gwamna Ortom ya yi addu’ar Allah ya ba wa ruhin Olajide Sowore hutawa ta har abada, ya kuma ba danginsa ƙarfin juriyar wannan rashin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *