fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Gwamna Zulum ya amince da biyan N624m a matsayin tallafi ga daliban makarantar gaba sakandaren a jihar Borno

A yayin da za’a sake bude manya makarantu a jihar Borno a ranar Litinin, Gwamna Babagana Zulum ya amince da fitar da Naira miliyan 624 don biyan kudin tallafin karatu ga daliban manyan makarantu a jihar.

 

Kwamishinan Ilimi mai zurfi, Kimiyya, Fasaha da Innovation, Dr Babagana Mustapha ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Maiduguri. Mustapha ya ce ɗalibai 23,776 daga cibiyoyi 49 za su ci gajiyar wannan tallafin.

 

Ya kara da cewa tuni aka saki kason farko na Naira miliyan 320 aka biya wa daliban cibiyoyi tara, ya kara da cewa sauran daliban za su samu nasu ne daga Litinin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *