fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Gwamna Zulum ya bayar da umurnin gina gidaje 500 ga yan gudun hijira a Nguro Soye

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bada umarnin a gina gidaje 500 a Nguro Soye, dake Karamar Hukumar Nana ga mutanen da muhallinsu a sanadiyyar tashe-tashen hankula.

Bugu da kari, gidaje masu zaman kansu 1,000 a garin wadanda maharan suka lalata za a gyara su.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin ziyarar da ya kai jiya a garin Bama, yayin da yake a fadar Shehun Bama, Shehu Umar Ibn Kyari Ibrahim El-kenemi.

Zulum ya kuma yi alkawarin kara samar da damar samun ilimin jama’a ga duk yaran da suka isa shiga makaranta.

Gwamnan ya kuma amince da bukatar Shehun Bama na karin tallafin ga manoma gabanin lokacin damina.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *