fbpx
Friday, May 14
Shadow

Gwamnan Jihar Ebonyi ya tsallake Rijiya da baya yayin da ‘yan Bindiga suka bude wuta

‘Yan bindiga sun bude wuta a kusa da inda za’a gina Filin jirgin Sama na jihar Ebonyi inda ake wani aiki.

 

‘Yan Bindigar da Rahotanni suka bayyana cewa sun je akan Babura 7 da motoci 2 sun tarar da Kwamishinan ayyuka na jihar, Engr Fidelis Nweze inda yayi ta kansa.

 

Rahoton yace ‘yan Bindigar sun yi tsammanin Gwamnan ne zai je ganin aikin da ake yi, shiyasa suka masa wannan Shiri. Saidai duk da haka, sun yi harbi a iska, inda daga baya suka fice daga wajan.

Saidai da yake magana akan harin, Kwamishina, Engr Fidelis Nweze ya bayyana cewa ba gaskiya bane wai ‘yan Bindigar Gwamna suka so kaiwa hari ba, kawai dai sun kai harin ne kamar yanda suka saba, yace dalilin da yasa ake alakanta harin da Gwamna, Siyasa ce kawai da aka saba alakanta duk wani abu da ya faru dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *