fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Gwamnan Jihar Gombe ya  sauke kwamishinoninsa 3

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sauke wasu Kwamishinoninsa guda uku.

Kwamishinonin da aka sallama din sun hada da Alhassan Ibrahim Kwami – bangaren yada labarai da al’adu, Dakta Ahmed Mohammed Gana- Lafiya da Mela Audu Nunghe (SAN) – Ayyuka na Musamman.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Njodi wanda ya sanar da hakan a ranar Litinin 1 ga Maris, ya kara da cewa an sake sauya wa kwamishinoni shida zuwa wasu ma’aikatun.

Tuni gwamnan zabi wasu mutane 33 da yake jira majalisar dokokin jihar ta tabbatar da nadin su a matsayin wadanda za su maye gurbin wadanda aka sauya daga aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *