fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Gwamnan jihar Nasarawa ya kori kwamishinoni da masu rike da mukaman siyasa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kori dukkan membobin majalisar zartarwa ta jihar.

Gwamnan ya sanar da korar ne a karshen wani babban taro da aka yi a gidan gwamnati ranar Litinin, a Lafiya.

Jim kadan bayan sanar da korar, Sule ya nuna godiya ga duk masu rike da mukaman siyasa saboda sadaukarwar da suka yi wajen tabbatar da isar da alkawuran yakin neman zabensa ga mutanen jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Daga nan ya umarci dukkan masu ba da shawara na musamman, mataimaka na musamman da manyan mataimaka na musamman, da su bar ofisoshin su.

Duk da cewa ba a bayar da dalilin korar ba, wata majiyar gwamnati da ta nemi a sakaya sunanta saboda tsoron ramuwar gayya ta ce “Duk mun san cewa mafi yawan mataimakan musamman na siyasa ya dauke su ne bisa shawarar tsoffin gwamnonin jihar da suka gabata.

“Don haka, na yi imanin ya sallamar su ne don shigar da nasa kafar sa cikin tsarin siyasa kafin fara zaben kananan hukumomi a ranar 6 ga watan Oktoba da zaben gwamna a 2023 saboda yana samun karbuwa a fadin jihar don ci gaba da zama gwamna. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *