fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Gwamnan jihar Yobe, Buni ya jinjinawa sojojin suka dakile harin Boko Haram a Geidam

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya jinjinawa sojoji karkashin Operations Hadin Kai saboda jaruntakar da suka nuna wajen tunkararwa da kuma dakile yunkurin kai hari garin Geidam jiya da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi.

Gwamna Buni a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed ya fitar a ranar Alhamis, ya kuma jinjina wa Kwamandan da ya tattara mutanensa suka fice daga Geidam don fuskantar abokan gaba a bayan garin.

“Abin farin ciki ne cewa, duk da cewa abokan gaba sun ja da baya, sojojin sun bi su da farin ciki kuma sun fatattaki ‘yan kwanto da ke kan hanyarsu.

“Gwamnati da jama’ar jihar Yobe sun yaba da wannan aikin bajinta don tabbatar da yankin baki daya da kuma ba mutanen Geidam damar ci gaba da bukukuwan Sallah cikin lumana”, in ji Gwamnan.

Buni ya bayyana cewa irin wadannan matakan za su magance hare-haren wuce gona da iri kan al’ummomin da ba su ji ba su gani ba.

Ya yi kira ga jama’a da su ba da gudummawa don ba da bayanai masu amfani a kan lokaci zuwa ga jami’an tsaro don inganta matakan magance wadannan hare-hare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *