fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Gwamnan jihar Zamfara ya fito da sabuwar dabarar yaki da ‘yan Bindiga

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa, zai yi amfani da cibiyoyin tattara bayanai da ma’aikatar sadarwa ta samar a jihar wajan yaki da ‘yan Bindiga.

 

Gwamnan yayi magana ta bakin daraktan yada labaransa, malam Yusuf Idris Gusau inda yace, gwamnan ya fadi hakane yayin ziyarar da ya kaiwa Sheikh Isa Ali Pantami ranar Laraba a Ofishinsa dake Abuja.

 

Gwamnan yace zai yi amfani da cibiyoyin tattara bayanan dan ganin cewa an cimma dalilin kafasu.

 

Gwamnan ya kara da cewa, Fasahar Zamani na Tasiri sosai wajan yaki da ta’addanci a Duniya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *