fbpx
Monday, November 29
Shadow

Gwamnan Najeriya ya nemi shugaba Buhari ya halasta Noman Tabar Wiwi a ganawar da suka yi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jiya, Talata ya gana da gwamnan Jihar Ondo,Rotimi Akeredolu a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja. Akwai rade-radin dake cewa Sun tattauna akan maganar dakarun Amotekunne amma Akeredolu ya musanta wannan magana.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Akeredolu wanda shine shugaban gwamnonin Kudu maso yanna ya bayyana cewa kamin ganawarshi da shugaba Buhari ya karanta a wasu jaridu cewa zai gana da Buharin akan maganar jami’an Amotekun, yace wannan daliline yasa ddole ya warware maganar.

Yace basubyi maganar Amotekun da shugaba Buhari ba, hakanan shima shugaban bai taso mai da maganar ba dan ba abinda ya kaishi kenan ba, yace ya je ganawar da shugaba Buhari ne dan ya gayyaceshi zuwa bude gadar sama ta Biliyan 5 da gwamnatinshi ta gina.

Da aka tambayeshi maganar ko yayi amfani da damar Amotekunne wajan neman sake cin zabe a karo na 2,sai yace ba haka zancen yake ba, abinda yayi a Ondo a bayyane yake ga kowa ya gani kuma zuciyar mutanen jiharshi na tare dashi.

Ya ce ya kuma yi amfani da ganawar da shugaban kasa dan neman halasta noman Tabar Wiwi, yace ba wai dan yana shan ta ba, amma dai yana amfani da man CBD da ake samarwa daga Wiwi din.

Ya kara da cewa, yasan irin afanin Wiwi din ta bangaren kiwon Lafiya da kuma tattalin arziki shiyasa yake son a halasta Nomanta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *