fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Gwamnan Zamfara ya sanar da sakin Mutane Hudu da akayi garkuwa da su a jihar

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake samun nasarar hanyar sakin wasu mutane da akayi garkuwa da su hudu ba tare da kudin fansa ba.
Wadanda aka sace wadanda aka kwashe kwanaki 49 ana tsare da su, sun ce an sace su ne a yankin Boko da ke karamar hukumar Zurmi.
Daga cikin su akwai Hakimi da kuma kansila mai ci a karamar hukumar Zurmi ta jihar.
Wannan na zuwa ne kusan makonni uku bayan da gwamnatin jihar ta ba da damar sakin wasu mazauna jihar 10 da aka sace.
Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga ‘yan fashin kafin a sako mutanen.
A ranar 9 ga Maris, gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Abubakar Dauran, ta sanar da cewa wadanda aka yi garkuwar da su tsawon sama da watanni uku da makonni biyu an sace su ne a yankin Gwaram da ke karamar Hukumar Talata Mafara ta jihar.
Daga cikinsu akwai maza uku, ciki har da mahaifin daya daga cikin ‘Yan matan Makarantar Jangebe da aka sace, mata hudu da yara uku.
Dauran, ya ce an kubutar da su ba tare da kudin fansa ba ta hanyar shirin zaman lafiya na gwamnatin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tattaunawar zaman lafiya, yana mai cewa hakan hanya ce da za ta samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *