fbpx
Monday, October 25
Shadow

Gwamnati tace dole kowane ma’aikaci yayi rigakagin Coronavirus

Gwamnatin Najeriya za ta hana duk wani ma’aikacin gwamnati da ba a yiwa rigakafin korona ba shiga ofis daga ranar 1 ga watan Disamba.

Sakataren Gwamnatin kasar wanda shi ke jagorantar kwamitin Shugaban kasa kan yaki da Korona Boss Mustapha ne ya bada sanarwar, a wani zama da kwamitin yayi a Abuja yau Laraba.

Jaridar Daily Trust ta ambato wani bangare na sanarwar na cewa ” daga ranar 1 ga watan Disambar 2021, gwamnatin tarayya za ta bukaci ma’aikatanta su nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafi ko kuma sakamakon da ke nuna cewa ba su dauke da cutar wanda bai wuce awa 72 ba kafin su shiga ofis.”

A cewar Sakataren Gwamnatin, kididdigar gwaji ta sama da makonni hudu da suka wuce ta nuna cewa yayin da bazuwar cutar ke raguwa a wasu jihohi, tana karuwa ne a wasu jihohin.

A wata mai kama da haka kwamitin ya sanar da janye dokar hana shiga kasashen Afrika ta Kudu da Turkiyya da kuma Brazil, wadanda a watan Mayu ta saka su cikin jerin kasashe da ke da hadari sosai saboda bazuwar korona a can.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *