fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Gwamnatin Borno da al’ummarta na cikin ‘fargaba’ kan sakin tubabbun ƴan Boko Haram

Gwamnatin Borno da al’ummarta na cikin damuwa kan sakin tubabbun mayaƙan Boko Haram 565 da mahukunta sojoji suka yi.

Wasu mazauna Maiduguri da mutanen da rikici ya raba da matsugunansu kuma ke rayuwa yanzu a sansanonin ‘yan gudun hijira sun ce sun kadu sosai lokacin da suka samu labari daga Abuja cewa an saki tubabun mayakan Boko Haram.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa al’ummar Borno na nuna damuwa kan abin da ya sa za a saki mayaƙan da suka mika wuya cikin ‘yan makonni da suka gabata, ganin cewa sun shafe shekara da shekaru suna ta’addanci.

A nata ɓangaren gwamnati Borno ta ce har yanzu ba ta da cikakkiyar masaniya kan ci gaban da aka samu ko sakin mayaƙan.

Sai dai wasu majiyoyin da ke kusa da gwamnati na cewa babu tattaunawa ko tuntubar juna tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Borno kafin sakin mayaƙan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *