fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Gwamnatin Buhari ta kwato Naira tirliyan daya da aka sace>>Shugabannin APC

Wasu shugabannin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya sun ce kimanin niara tirliyan guda da aka sace ciki har da kadarori gwamnatin Buhari ta kwato daga lokacin da ta karbi mulki a 2015.

A wata sanarwa da ta suka fitar a ranar Alhamis, tsohon kakain sakataren jam’iyyar Mr. Lanre Issa-Onilu; da mamban na kwamitin rikon kwarya Barista Ismail Ahmed, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Mr. Tolu Ogunlesi da kuma babban daraktan shirye-shiryen zauren gwamnoni Salihu Lukman an kwato kayan ne daga 2015 zuwa yanzu.

A cewar sanarwar, duka dukiyar da aka kwace an rika amfani da ita ne a ayyukan gwamnati na raya kasa da kuma na taimakon al’umma ko kuma an cike gibin kasafin kudi na shekara shekara.

Jaridar Daily Trust shugabannin APC karkashin inuwar (APC Legacy Awareness and Campaign) bugu da kari kan kudaden da aka sace aka boye, gwmanatin Buhari ta mayar da hankali kan tabbatar da ana karbar haraji da kuma karbo wasu basuka da gwamnatin tarayyar ke bi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *