fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Gwamnatin Jihar Anambra ta sanya dokar hana fita a kan al’ummar Igbariam, Aguleri, Umueri, Nteje, Awkuzu da Umunya bayan an kashe mutane 9

Gwamnatin jihar Anambra ta sanya dokar hana fita a kan wasu garuruwan 6 na Anambra bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe mutane 9 tare da jikkata wasu.

An sanya dokar hana fita a kan Igbariam, Aguleri, Umueri, Nteje, Awkuzu Da Umunya.

A cikin wata sanarwa, Sakataren gwamnatin jihar Anambra, Farfesa Solo Chukwulobelu ya ce dokar hana zirga-zirgar za ta fara ne daga ranar Litinin, 26 ga Afrilu, 2021, kuma za ta kasance tsakanin 7 na yamma zuwa 6 na safe a kowace rana.

Sanarwar ta shawarci ‘yan asalin Anambra da mazauna jihar da ke zaune a cikin wadannan al’ummomi da su yi biyayya ga dokar hana fita, saboda jami’an tsaro suna kan tsauraran umarni don aiwatar da dokar.

An ba da rahoton cewa mazauna da ɗalibai a cikin al’ummomin da abin ya shafa suna fara kaura saboda su tsira da rayukansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *