fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Gwamnatin Jihar Filato ta hana shuka masara da duk wani abu mai tsayi a cikin garin

Janar Manaja, Hukumar Kare Muhalli da Tsabtace Muhalli ta Filato, PEPSA, Gabriel Bako, ya ce dokar da ke haramta dasa masara da dogayen kayan gona a wuraren zama na babban birnin na ci gaba da aiki.

Mista Bako ya fadawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya a Jos cewa shuka dogayen kayan gona kamar an yiwa sauro da bera wurin zama ne.

Ya kuma gargadi mazauna cikin garin Jos-Bukuru da su guji zubar da shara a magudanan ruwa, da kuma yin gini a kan hanyoyin ruwa saboda ayyukan na haifar da barazanar ga lafiya da kuma ambaliyar ruwa ga al’ummar yankin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *