fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Gwamnatin jihar Kaduna ta sallami ma’aikatan kananan hukumomi

Ma’aikatan Sakatariyar karamar hukumar Jema’a su 82 da ke Kafanchan a Kaduna aka sallama daga aiki.
Sun karbi wasikun sallamarsu daga gwamnatin jihar a ranar Laraba, NAN ta ruwaito.
Wannan ci gaban ya biyo bayan rade-radin cewa gwamnatin Nasir El-Rufai na shirin rage yawan ma’aikatanta a cikin kananan hukumomi 23.
Wasikar ta bayyana cewa hakan ya yi daidai da yadda ake ci gaba da sake fasalin kananan hukumoni domin a samu saukin aiki.
“Me yasa gwamnatin jihar ke mana haka yanzu? Shin ba su san mawuyacin lokacin da muke ciki a matsayinmu na yan ƙasa ba? ”, Ma’aikatan da abin ya shafa suka kuka.
Ajayi Chiroma, wanda ya rage masu shekara biyar a aiki, ya yi kira da a hanzarta biyan su kudadensu kamar yadda wasikar ta bayyana.
“Ina fatan za su biya mana hakkokinmu nan ba da dadewa ba saboda wannan ne kawai abin da za mu koma baya a kansa”, in ji shi.
“Ba fiye da mutane 82 abin ya shafa ba”, Mataimakin Shugaban kamar hukumar Jema’a, Micah Ngboni ya tabbatar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *