fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Gwamnatin jihar Kano ta kulle wani gurin ajiyar kayayyakin abinci na jabu

Kwamitin rundunar tsaro na jihar Kano kan jabun magunguna da sauran kayan masarufi, inda suka rufe wani sito a yankin Bompai da ke cikin garin Kano da manyan motoci biyu dauke da kayan da ake zargin na jabu ne.

Kwamitin ya bayyana cewa kayayyakin da aka kama galibinsu abubuwan sha ne.
Da yake magana kan rufe shagon, Shugaban kwamitin, Dokta Ghali Sule, ya ce an gano hakan ne bayan da aka kama wata motar da ke dauke da wasu kayayyakin abinci da ake zargi daga wurin ajiyar ne.
Sule ya jaddada kudirin kwamitin har ila yau n fitar da jihar daga magunguna marasa inganci, wadanda ke haifar da hadari ga lafiyar mutane.
A nasa bangaren, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Aminu Tsanyawa, ya sake jaddada aniyar ma’aikatar na dakatar da yaduwar magunguna na jabu da marasa inganci da kayayyakin abinci a cikin jihar.
Ya ce yayin da lokacin azumin Ramadan ya gabato, wasu ‘yan kasuwa suna amfani da babbar bukatar kayan masarufi don aikata ayyukan da ba su dace ba don samun kudi ta kowace hanya.
Ya ci gaba da cewa, ma’aikatar, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), nan ba da dadewa ba za su fara bincike don gano asalin kayayyakin na jabu da marasa inganci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *