fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Gwamnatin Jihar Neja ta umarci makarantu da su koma bakin aiki a ranar 25 ga watan Janairu

Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta gyara Manhajar zangon karatu na shekarar 2020/2021 inda wa’adin farko, zai fara daga ranar Litinin, 4 ga Janairu, 2021,Wanda a yanzu sabuwar ranar zata kasance ranar Litinin, 25 ga watan Janairun 2021, tana mai cewa sabuwar ranar ita ce ranar da za a dawo da ayyukan ilimi a duk makarantun firamare da sakandare a jihar.

Kwamishina, Ma’aikatar Ilimi, Hajiya Hannatu Jibrin Salihu ce ta bayyana hakan a karshen mako yayin da take tattaunawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar.

Hakanan kwamishinan ta bukaci Makarantu dasu bi ka’idojin cutar Covid-19 wajan sanya ta kunkumin rufe hanci, wanke hannaye, da kuma bada tazara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *