fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Gwamnatin jihar Ondo ta kwato motoci uku daga hannun tsohon Mataimakin Gwamnan

Gwamnatin Jihar Ondo ta kwato motoci uku a hannun tsohon Mataimakin Gwamnan, Agboola Ajayi.

Motocin sun hada da Toyota Landcruiser Jeep, V8, samfurin 2019 da kuma Toyota Hilux motoci guda biyu suma na samfurin 2019.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Donald Ojogo, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 26 ga Afrilu, ya ce yayin da ake kokarin dawo da duk sauran motocin da suka rage da ke hannun tsohon Mataimakin Gwamnan, Gwamnati na nuna godiya ga hukumomin tsaro, musamman ‘yan sanda, akan namijin Kokari da suka yi.

Wannan ci gaban na zuwa ne kusan makonni biyu bayan da Gwamnatin Jiha ta nemi ‘yan sanda ta su matsawa Ajayi, don dawo da motocin gwamnati dake hannun sa watanni biyu bayan fitar sa daga ofis.

Odebowale ya koka cewa Ajayi har yanzu yana rike da motocin gwamnati guda hudu duk da cewa ya bar ofis kusan watanni biyu da suka gabata, yana mai cewa duk da rokon da ake yi masa na ya dawo da motocin don sabon mataimakin gwamna mai ci yayi amfani da su amma yaki amincewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *