fbpx
Friday, May 14
Shadow

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana yadda suka kwato shanu 300 yayin dakile harin ‘yan bindiga a jihar

Bello Matawalle, gwamnan Zamfara, ya ce jami’an tsaro a jihar sun kashe wasu gungun ‘yan bindiga tare da kwato shanu 300 daga hannun su.

Matawalle ya lura cewa yan fashin sun sace garken shanu sama da 300 a Kuraje kusa da Rijiyar Tsakar Dawa a karamar hukumar Gusau.
Gwamnan, a cikin wasu sakonnin twitter a ranar Lahadi tare da hotunan da ke nuna shanu da aka kwato, ya ce tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida sun gudanar da aikin kubutar da su.
Ya ce an dawo da shanun da aka kwato ga masu su, yayin da ya tabbatar wa mazauna kudirin gwamnatinsa na maido da zaman lafiya a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *