fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Gwamnatin Kano ta ɗauki ƴan ƙoroso 45 aiki na din-din-din

Gwamnatin Kano ta raba takardar ɗaukar aiki na din-din-din ga ƴan rawar ƙoroso 45 da su ke aikin wucin gadi a Ma’aikatar adana Tarihi da Al’adu ta jihar.

Da ya ke raba takardun ɗaukar aikin a ɗakin taro na ma’aikatar, Kwamishinan Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Ibrahim Ahmed Karaye ya ce aikin wani yunƙuri ne na gwamnatin Abdullahi Ganduje wajen sakawa ma’aikata na wucin-gadi da su ka bada gudunmawar su wajen ci gaban jihar.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Ganduje ta dage wajen sauƙaƙa rayuwar al’umma ta hanyar samar da aiyukan ci gaba da shirye-shirye da za su amfani jama’a kai tsaye.

Kwamishinan ya ja hankalin ma’aikatan da su yi amfani da wannan dama wajen bunƙasa al’adun Hausawa da jihar Kano a duk inda su ka je aiki.

Ƙaraye ya yiwa ƴan ƙoroson alƙawarin cewa shirye-shirye sun yi nisa 2ajen samar musu da kayan sawa na-gani-na-faɗa yadda za su riƙa cinyewa a duk inda su ka je yin wasa.

Ya kuma yi kira gare su da su goyawa gwamnatin Ganduje baya a ko da yaushe.

Daily Nigerian Hausa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *