fbpx
Monday, September 27
Shadow

Gwamnatin Kano ta hana sayar wa ko ba da hayar gidaje ba tare da saninta ba

Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin cewa daga yanzu babu wani gida ko fili da za a sayar ko a bayar da haya a jihar ga wani mutum ko kungiya ba tare sahalewar dagaci ko kuma wasu wakilai da aka aminta da su ba a hukumance.

Cikin wata sanarwa da kakakin sakataren gwamnatin ya fitar Musa Tanko Muhammad, ya ce an dauki wannan mataki ne saboda tabbatar da aminci da kuma tsare rayukan da dukiyoyin mutan jihar Kano.

Ya ce wannan mataki ya zama dole ne domin tabbatar da cewa ayyukan da sojojin Najeriya ke yi na fatattakar ‘yan fashin daji a wasu sassan kasar ya tafi daidai.

Ya kara da cewa matakin na tafiya kafada da kafada da abin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba na kawo karshen matsalar rashin tsaro da kuma ‘yan bindiga a wasu sassan kasar, lokacin da ‘yan bindigar ke fama da wahala to suna tsallaka wa jihohin da ke makwabtaka ciki kuma har da Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *