fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Gwamnatin Kano ta karyata rade-radin dake yawo cewa Coronavirus/COVID-19 ta shiga jihar

Gwamnatin jihar Kano ta karyata rade-radin dake yawo cewa wai an samu me Coronavirus/COVID-19 amma gwamnatin na rufa-Rufa.

 

Wannine yawa Hadimin gwamnan Kano,Salihu Tanko Yakasai tambaya kan lamarin inda shi kuma ya bashi amsar cewa ba gaskiya bane.

 

Yakasai yace gwamnati ba zata yi wasa da rayuwar mutane ba ta boye cutar idandai an tabbatat da ita.

 

Da yake magana akan saka dokar hana fita kwata-kwata, Yakasai yace mahukunta sun lura cewa idan aka saka dokar hana zirga-Zirga a Kano ba tare da an samu cutar ta shiga jihar ba to za’a takurawa talakawane.

 

 

 

Gwamnatin Kano na ci gaba da daukar matakan rigakafi dan ganin cewa cutar bata shiga jihar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *