fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Gwamnatin Kano ta kori wani ma’aikacin lafiyar bisa laifin fyade tare da wasu ma’aikata 3

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano, PHCMB, ta sallami wani ma’aikata a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Kurnar Asabe bayan an same shi da laifin fyade.

Kwamitin, a cikin wata sanarwa da kakakinta, Maikudi Marafa, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, wadda bai bayyana sunan ma’aikacin ba amma ya bayyana lambar sa ta aiki KNLG 32323.

Kwamitin ya kara da cewa an kori wasu ma’aikata biyu masu lambar aiki KNLG 09068 da KNLG 018423 daga Karamar Hukumar Gezawa bayan an same su da laifin amfani da bayanan ma’aikata wajen karbar rance ba tare da yardar su ba.

Sauran ma’aikacin da hukumar ta PHCMB ta sallama, tare da KNLG 04608 daga Karamar Hukumar Gwarzo, an zarge shi da gudanar da aikin zubar da ciki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *