fbpx
Monday, September 27
Shadow

Gwamnatin Kano ta musanta cewa tana da shirin hana mata tukin mota

Wani sako da aka rika yadawa a shafukan sada zumunta da ke ikirarin cewa wasu malaman Kano da ke arewacin Najeriya sun nemi gwamnatin jihar ta hana mata tuka mota ya dauki hankalin jama’a.

Sakon ya yi ikirarin cewa gwamnatin Kano da Majalisar Malaman jihar na shirin kafa dokar da za ta hana mata daga ko wanne addini tuka mota.

Sai dai gwamnatin jihar da ma malaman sun ce wannan ikirarin ba shi da kanshin gaskiya.

Wannan sako, wanda mutane da dama suka rika yin tsokaci a kansa a shafukan sada zumunta, ya ce an yanke shawarar ce a wani taron sirri da aka gudanar a Hukumar Shari’a ta jihar Kano tsakanin Kwamishinan Harkokin Addinai Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) da wata tawagar malaman jihar wadda Sheikh Abdulwahab Abdallah BUK ya jagoranta.

Sakon ya ce “tuni ake dab da kammala wani daftarin doka a Ma’aikatar Shari’ar jihar wanda zai hana mata mota kuma ko wanne lokaci daga yanzu za a iya gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin jihar domin mayar da shi doka.”A cewar sakon, fitaccen malamin nan na jihar ta Sheikh Abdallah Usman Umar Gadon Kaya, yana yin uwa-da-makarbiya wajen ganin an hana mata tuka mota saboda “kyale mata su yi tuki wani abin wadarai ne a rayuwarmu a matsayin Musulmai.”

Sai dai malamin ya fito fili ya karyata wannan zargi.

Tun da farko, in ji sakon, Kwamishin Harkokin Addinai, Baba Impossible, ya tabbatar wa malaman cewa Gwamna Ganduje zai yi bakin kokarinsa wajen kawar da ayyukan masha’a a jihar.Shi ma Kwamandan Hisbah, Ustaz Harun Mohammad Ibn Sina ya ce za su tabbatar da bin dokar idan aka kaddamar da ita, a cewar sakon.

Sai dai Kwamishinan Harkokin Addinai na jihar Kano, Muhammad Tahar Adamu, ya shaida wa BBC Hausa cewa babu kanshin gaskiya a sakon da ake ta yadawa.

Ya ce kamar kowa, shi ma ya ga sakon kuma abokan aikinsa Kwamishinoni, sun rika tambayarsa kan lamarin a wurin taron majalalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar ranar Laraba amma ya gaya musu cewa labarin kanzon-kurege ne.

Shi ma fitaccen malami Dr Abdallah Usman Umar Gadon Kaya ya fitar da wani sakon murya inda yake musanta wannan labari yana mai cewa wasu makiyansu ne suke watsa shi.

“Amsa dangane da wannan tambaya da aka yi min… cewa wasu malamai sun zauna da wasu jami’ai na gwamnati a Kano a Shari’a Commission an fid da kudurin cewa wai za a fitar da wata dokar, ko za a sa gwamnati ta hana mata tuki;

Har ma a cikin takardar ake cewa ni Dr Abdallah Usman Umar Gadon Kaya ni na zo da kudurin…wannan magana, wannan takarda da aka yada ba ta da tushe ba ta da asali,” in ji shi.

Malamin ya kara da cewa maganar “karya ce tsagwaronta. Wallahi tallahi ba mu san da ita ba. Wallahi tallahi ba a taba yin wani zama makamancin wannan ba.”

Dr Gadon Kaya ya ce malaman Kano ba su da ra’ayin hana mata yin tuki yana mai yin kira ga al’ummar jihar su guji masu yada irin wadannan labarai na karya.

Sheikh Gadon Kaya ce shi da sauran malaman da ake zargi da hannu a cikin lamarin sun fito kafafen sada zumunta sun nesanta kansu daga batun.

Ya kara da cewa wasu ne da suka ga yadda suke kokarin kare martbar Manzon Allah (SAW) suke yada irin wadannan karairayi da neman bata sunansu “da kokarin jefa kiyayyarmu a zukatan mutane.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *