fbpx
Monday, September 27
Shadow

Gwamnatin Taliban za ta raba ajin mata da maza a jami’oin Afghanistan

Kungiyar Taliban ta ce za a raba ajin mata da na maza a jami’oi, tare da bullo da irin shigar da mata za su rinka yi.

Ministan da ke kula da manyan makarantu a Afghanistan, Abdul Baqi Haqqani, ya bayyana cewa za a bar mata su ci gaba da karatun jami’a amma ba tare da zama wuri guda da maza ba.

Ministan ya kuma sanar da darussan da za a rinka koya wa dalibai.

A baya a lokacin da kungiyar Taliban ke mulki a Afghanistan wato a tsakanin shekarun 1996 zuwa 2001, mata ba sa zuwa makaranta.

A wannan karon Taliban ta ce ba za a hana mata neman ilimi ko samun aiki ba, amma tun bayan da suka karbi mulki a ranar 15 ga watan Augustan, 2021, aka dakatar da dukkan mata daga zuwa aiki sai wadanda ke aiki a bangaren lafiya kadai har sai yanayin tsaro ya inganta a kasar.

Sabbin manufofin da kungiyar ta bullo da su musamman a kan mata sun sha bamban da na gwamnatin da ta shude inda babu wani nau’in shiga da aka ware wa mata ko kuma raba su aji da maza.

Mr Haqqani ya ce: “Ba mu da wata matsala ko da-na-sanin raba mata da maza daga zama waje guda a jami’oi, saboda dukkaninmu musulmai ne, kuma koa ya san haka.”

Mutane da dama dai na ganin cewa wannan mataki na Taliban din zai iya hana mata samun ilimi saboda babu ajujuwa da malamai da dama a makarantun, sao dai Mr Haqqani ya ce tun da akwai malamai mata komai zai tafi yadda ake bukata.

Ya ce: “Idan ma malamai matan ba za su isa ba, to malamai maza za su iya koyar da mata amma sai an sanya labule ta yadda malamin ba zai ga fuskokin daliban ba idan yana koyar da su, koma a yi amfani da wata fasahar zamani wajen koyar da su.”

Kazalika za a raba dalibai mata da zama ma a makarantun firamare dana sakandire wanda wannan ba wani sabon abu bane a Afghanistan.

Baya ga raba daliban, za a umarci dalibai mata da su rinka sanya hijabi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *