fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Gwamnatin tarayya da wasu ‘yan Najeriya sun koma amfani da shafin Koo Indiyawa ke amfani dashi wajan nuna kiyayya ga Musulmai

Gwamnatin tarayya da wasu ma’aikatunta sun fice saga shafin Twitter inda suka koma amfani da shafin Koo mallakin kasar India.

 

Hakanan wasu ‘yan Najeriya da suka amince da da daina Amfani da Twitter suma sun koma amfani fa shafin na Koo.

 

Saidai wannan shafi an kirkireshi ne bayan da aka samu rashin jituwa tsakanin kasar India da Twitter.  Hakanan ana ganin cewa, Shafin na kwaikwayar ayyukan Twitter ne in banda wasu abubuwa da ba za’a rasaba.

 

Amma wani abu da ya bayyana a shafin shine yanda ake nunawa Musulmai kiyayya, wanda sune marasa rinjaye a kasar India.

 

Akwai cin zarafi da kyama karara da ake nunawa Musulmai a shafin. Ana kuma yiwa musulmai kage da sharri a shafin, kamar yanda Peoplesgazette ta bayyana.

 

Misali an rika yada cewa, musulmai a kasar India na tofawa mutane yawu a abinci dan su yada cuta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *