fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Gwamnatin tarayya ta baiwa jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisin fara aiki

Gwamnatin tarayya ta baiwa jami’o’i 20 masu zaman kansu da a kwanakin baya ta amince da kafa su lasisin fara aiki.

 

An baiwa jami’o’in lasisin fara aikin ne a ranar Alhamis a babban Birnin tarayya, Abuja. hakan ya kawo yawan jami’o’in da ake dasu masu zaman kansu zuwa 99.

 

A watan Fabrairu da ya gabata ne, majalisar Koli ta tarayya ta amince da kafa jami’o’in.

 

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayyana cewa bude jami’o’in masu zaman kansu zai taimaka wajan bunkasar Ilimi, musamman ganin yanda jama’ar Najeriya ke karuwa. Yace za’a ci gaba da bude karin jami’o’i yayin da ake samun yawaitar jama’a.

 

Jami’o’in da aka bud sune kamar haka:

Topfaith University Mkpatak, Akwa Ibom; Thomas Adewumi University, Oko-Irese, Kwara; Maranatha University, Mgbidi, Imo; Ave Maria University, Piyanko, Nasarawa; Al-Istiqama University, Sumaila, Kano, Mudiame University, Irrua, Edo; Havilla University, Nde-Ikom, Cross River; Claretian University of Nigeria, Nekede, Imo, NOK University, Kachia, Kaduna, Karl-Kumm University, Vom, Plateau, James Hope University, Lagos, Maryam Abacha American University of Nigeria, Kano, Capital City University, Kano, Ahman Pategi University, Kwara, University of Offa, Kwara, Mewar University, Masaka, Nasarawa; Edusoko University, Bida, Niger; Philomath University, Kuje, Abuja; Khadija University, Majia, Jigawa and Anan University, Kwall, Plateau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *