fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta fara Gina Ƙarin Makarantu a Arewa maso Gabas

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta fara gina karin makarantu a Yobe da sauran sassan Arewa maso gabas.

An tattaro cewa gwamnatin Yobe ta bayar da fili don gina sabbin makarantun firamare da sakandare a kananan hukumomin Potsdam, Buni Yadi (Gujba) da Gahsua (Bade).

Manajan Daraktan hukumar, Mohammed Alkali, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar a Gasua, ya bayyana cewa shirin an yi shi ne don magance matsalar karancin azuzuwa da makarantu da yankin ke fama.

Ya kuma bayyana cewa, matsalar karancin makarantun firamare da sakandare a yankin Arewa maso gabas ya samo asali ne daga hare-haren masu tayar da kayar baya.

Ya kara da cewa rugujewar makarantu da maharan suka yi ya tarwatsa ilimin firamare da sakandare a yankin.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yabawa Gwamnatin Tarayya a kan wannan aikin da tasa a gaba domin magance matsalar ilimi a yankin. Haka ma yayi kira da masu hannu da shuni, sarakuna da saura jama’a akan su bayar da tasu gudumuwa domin samun ingataccen ilimi a yankin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *