fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da kamfanin Twitter

Najeriya ta ce tana tattaunawa da Twitter, bayan ta dakatar da amfani da kafar ta sada zumunta a ƙarshen mako.

Bayan ganawa da jami’an diflomasiyya, ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya ce gwamnatin za ta ga ci gaban da aka samu a tattaunawar kafin ta yanke hukunci.

A wani yunƙuri na baya-bayan nan kan Twitter, hukumomi sun umarci kafofin watsa labaran ƙasar su dakatar da amfani da shafukansu.

Jami’an diflomasiyyar kasashen yamma sun soki dakatarwar, suna masu fadin ‘yancin fadin albarkacin baki wani bangare ne na ci gaban dimokuradiyya.

Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa saboda an goge saƙon shugaba Buhari ne ya sa ta dakatar amfani da shafin Twitter.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *