fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Mahadi bisa zargin bata suna, tunzura jama’a a kan Gwamna Masari

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Muhammad Mahdi a gaban kuliya bisa zargin bata sunan gwamnan jihar Katsina, Bello Aminu Masari, gwamnatinsa da ta Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa.

An kuma tsare Mahadi bisa zargin tunzura jama’a game, a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kano.

Muhammad Mahdi wanda aka gurfanar da shi a kan tuhume-tuhume shida na zargin aikata laifuka ya musanta aikata dukkan laifukan.

Lauya mai shigar da kara, Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda, Simon Lough yayin gabatar da tuhume-tuhumen a gaban Kotu, ya zargi Muhammad Mahdi da zargin saba ka’idojin belinsa da kuma buga sabon labarin cin mutunci 32 daga Maris zuwa Yuni 28 2021, ga Gwamna Ballo Aminu Masari akan intanet.

Shari’ar mai taken, “Gwamnatin Tarayya da Muhammad Mahdi da Dialogue Global Ltd”, tana da tuhume-tuhume guda daya a kan Mahdi wanda ya zargi Masari da barnatar da Naira Biliyan 62 na Kudin Katsina.

Biyu daga tuhume-tuhumen sun yi zargin cewa Mahadi ya zargi Masari ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Rediyon Freedom na zargin almubazzaranci da Hukumar Tsaro ta Naira biliyan 64 na Jihar Katsina.

Idaya uku daga tuhume-tuhumen da suka shafi zargin da Mahadi ya yi wa Masari wanda ya zargi gwamnan ya amince da Naira miliyan 500 don taron APC a Abuja.

Bayan ya saurari dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa sosai, Muhammad Mahadi ya musanta laifukan duka.

Alkalin da ke jagorantar, Mai shari’a A. Lima ya dage sauraron karar zuwa 26 zuwa 27 ga Yulin 2021 don ci gaba da sauraro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *