fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta mika gidaje 1,000 ga ‘yan gudun hijira dake Jihar Borno

Gwamnatin tarayya a ranar alhamis ta mika gidaje 1,000 ga Gwamnatin Borno don rabawa ga ‘yan gudun hijira dake a kauyen Ngwom na karamar hukumar Mafa dake jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa gidajen da aka gina a karkashin Hukumar Raya Arewa maso Gabas, NEDC, na cikin tsarin gina gidaje 10,000 da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara.

Da yake jawabi a bikin, manajan daraktan NEDC, Mohammed Alkali, ya ce Shugaba Buhari a shekarar 2019 ya amince da aikin ginin gidaje a karkashin sa hannun Hukumar SPIB.

Shi ma da yake magana, Gwamna Babagana Zulum, ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan tallafin da take baiwa jihar, inda ya bayyana tallafin a matsayin karimcin da girmama.

Zulum ya ce wannan matakin zai yi saurin wajen taimaka wa yan gudun hijirar domin su koma gidajensu da suka gada tun kakanni da kakanni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *