fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Gwamnatin tarayya ta rage farashin Gas din da ake amfani dashi wajan samar da wutar Lantarki

Shugaban masa, Muhammadu Buhari ya bayyana rage farashin Gas din da ake amfani dashi wajan samar da wutar lantarki.

 

Shugaban ya bayyana hakane ta bakun karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva a jawabin da yayi a Kano.

 

Yace an rage farashin gas din daga $2.50 zuwa $2.18. Yace kuma an sanar da hukumomin da suka dace dan daukar matakin da ya kamata.

 

Da yake magana akan shinfida Bututun iskar gas daga Kogi zuwa Kaduna da Kano wanda akewa lakabi da AKK ya ce idan aka kammalashi zai farfado da masana’antu a jihohin Nasarawa Kaduna da Kano da kuma samarwa matasa aikin yi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *