fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Gwamnatin tarayya ta sanar da sabbin ma’aikatan N-Power Batch C Mataki na gaba da zasu bi

Gwamnatin tarayya ta sanar da Sabbin ma’aikatan N-Power na Batch C abinda ya kamata su yi.

 

Ministar Kula da Ibtila’i da Jinkai, Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana haka a ganawarta da manema labarai.

 

Tace kowa ya ajiye bayanansa kusa, dan nan gaba kadan za’a tuntubesu kan abinda zasu yi. Tace mutane 550,000 ne aka fitar da sunayensu. Kuma ana tuntubarsu a hankali.

 

Tace duk wanda ya samu aikin, zai je ya bada shaidar hannunsa dan ya samu kaiwa mataki na gaba, tace wanda ke neman wani bayani kuma yana iya kiran lambar waya, 0188883410,  08176551162. Ko kuma ya aika da Sakon Email ta [email protected] domin karin bayani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *