fbpx
Monday, September 27
Shadow

Gwamnatin Tarayya za ta dawo da miliyoyin nairori da aka biya likitoci 588 a bisa kuskure – Chris Ngige

Ministan Kwadago da Aiki, Chris Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kwato miliyoyin nairori da aka biya likitocin 588 ba bisa ka’ida a fadin kasar nan.

Ngige ya ce an gano sunayen likitocin da suka ci gajiyar fa’idar Asusun Horar da Ma’aikatan Lafiya don wani nau’in likitocin, bayan “cikakken bincike na sunaye 8000 da manyan daraktocin Likitoci na cibiyoyin lafiya na Gwamnatin Tarayya suka gabatar don shirin horon”.

Ministan wanda ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin likitocin da abin ya shafa sun dawo da makudan kudaden, ya kara da cewa an kara himma don dawo da sauran ragowar.

A cewarsa jinkirin da likitocin da abin ya shafa suka yi na dawo da kudaden, yana hana biyan kudin Asusun daga gwamnati.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake arangama tsakanin likitoci a kasar da gwamnatin tarayya kan yajin aikin da ke gudana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *