fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Gwamnatin Tarayya zata binciki yanda dan Najeriyar nan daya makale a tayar jirgin sama aka tafi dashi kasar waje har ya kai ga shiga ba tare da an ganshi ba

Dan Najeriyarnan da and a makale a tayar jirgin sama aka tafi dashi kasar Netherlands amma bai kai ba ya mutu za’a fara binciken yanda har ya sami zuwa wajan Jirgin ba tare da an ganshi ba.

 

Hukumar kula da Filayen Jiragen sama ta FAAN reshen kudu maso yamma tace za’ayi bincike kan lamarin. Daya daga cikin jami’an hikumar Victoria Shi-shan ta bayyana haka.

 

Ana sa ran mutumin ya makalene dan zuwa kasar waje ta barauniyar hanya. Kuma ya tashi daga filin jirgin sama na Legas ne.

 

Suma fai hukumomin kasar Netherlands din sunce suna bincike akan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

1 Comment

  • Lauwali manchester kamba

    Ba yadda za’ayi mutun ya shiga filin jirgin sama har ya maƙale ga taya ace ba wanda ya ganai,
    Gaskiya akwai sa hannun ma’aikatan filin jirgin dasu aka shirya,
    Akwai sa hannun wani ɓara gurbi daga cikin ma’aikatan nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *