fbpx
Friday, May 14
Shadow

Gwamnatin tarayya zata sayar da kamfanonin samar da wutar Lantarki

Gwamnatin tarayya ta sanar da Aniyarta ta sayar da Kamfanonin Wutar Lantarki inda har ta gayyaci kamfanoni masu sha’awar siye su mika takardun harama.

 

Kamfanonin guda 5 za’a sayar dasu ne a karkashin hukumar BPE. Daraktan Hukumar, Alex Oko ne ya sanarda haka.

 

Kamfanin Dillancin labaran Najeriya, NAN ya bayyana cewa hakan na daya daga cikin tsare-tsaren gyara a bangaren wutar Lantarkin.

Kamfanonin sune, Geregu Generation Company Ltd, Benin (Ihovbor) Generation Company Ltd,  507 MW, Calabar Generation Ltd, 634MW, Omotosho Generation Ltd, 513MW da Olorunsogo Generation Company Ltf, 754MW.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *