fbpx
Monday, November 29
Shadow

Gwamnatin Zamfara Ta Yi Alkawarin Bada Kyautar Naira Milyan Biyu Ga Duk Wanda Ya Kama Wanda Ke Jefa AL’KUR’ANI A Shadda

Gwamnan jihar Zamfara Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya samu rahoto daga Kwamitin da suka yi bincike akan wulakanta  Alqur’ani mai girma da wasu su kayi a jihar Zamfara.

Yayin da yake mayar da martani ga rahoton kwamitin, Gwamnan ya bada umarnin kafa doka nan take ta hanzarta zartar da hukunci a kan wadanda suka aiwatar da wannan aika aikar, don su kasance masu yin hanin faruwan hakan ga wasu.
Ya sake nanata tayin bayar da gagarumar kyauta ta kudi ga duk wanda zai iya samar da sahihan bayanan da za su kai ga kama, gurfanar da wadanda ake zargi da aikata hakan.
Ya kuma yi gargadi game da mummunan hukuncin Allah Madaukakin Sarki yana jiran mutane idan suna aikata mummunan aiki don wani abin duniya.   
Ya sake tabbatar wa da jama’ar jihar bisa shirye-shiryen gwamnatinsa na kare tsarkakan addinai da bayar da fifikon tsaro da zaman lafiyar al’umma da tattalin arzikinsu a koyaushe.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *