fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Gwamnoni ba su da cikakken iko don magance matsalar rashin tsaro>>Lalong

Simon Lalong, gwamnan Filato, ya ce akwai iyaka ga abin da gwamnonin jihohi za su iya yi game da rashin tsaro a kasar.
Ya koka kan yadda gwamnoni ba su da cikakken iko a kan jami’an tsaro a jihohinsu.
Lalong yayi magana ne a ranar Juma’a yayin shirin Good Morning Nigeria a Gidan Talabijin na Najeriya (NTA).
Ya ce duk da cewa kundin tsarin mulki ya sanya gwamnoni su zama manyan hafsoshin tsaron jihohinsu, amma akwai iyaka ga umarnin da za su iya ba jami’an tsaro.
Lalong ya yi kira ga majalisar kasa da ta sanya baki, ya kara da cewa ‘yan majalisar tarayya suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da an baiwa gwamnoni ikon magance matsalar rashin tsaro.
  • Lalong ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta magance matsalolin tsaro da kuma aiwatar da duk rahotonnin tsaro da aka tsara kuma aka gabatar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *