fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Gwmana Ganduje Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 136 A Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya aiwatar da sakin fursunoni 136 daga cibiyoyin kula da su a wani bangare na bikin Eid-el-Kabir.

Ganduje, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren sa na yada labarai, Abba Anwar, ya sanar da yafiyar ga ‘yan gidan yarin a ranar Talata lokacin da ya ziyarci Cibiyar ta Goron Dutse.

Gwamnan ya ce: “A matsayinku na’ yan Najeriya da suka cancanci a kula da su, muna nan a yau, ranar Sallah, don taya ku murna da wannan babbar lokacin Sallah, ta hanyar sakin wasu daga cikinku da aka yi musu afuwa.

“Mun zo ne don kuma ganin yadda kuke ji da kuma raba maku farin ciki tare da ku.

“Muna son wadanda suka tuba daga cikinku su yi alkawarin ba za su koma ga munanan ayyukansu na baya ba,” in ji shi.

Ya kuma bukaci fursunonin da aka ‘yanta su kasance masu halaye na kwarai idan aka  sake su cikin al’umma.

Da yake bayyana dalilan da ya sa aka sake su, Ganduje ya ce: “An sake wasu daga cikinku ne saboda rashin lafiya, wasu sun daɗe fiye da yadda ake buƙata wasu kuma an kulle su ne saboda ba su iya biyan kuɗin da aka ɗora musu.”

Amma, ya ci gaba da cewa aikin yafiya ya yi daidai da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga cibiyoyin kula da fursunoni a duk fadin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *