fbpx
Monday, September 27
Shadow

Gwmantin jihar Jigawa ta mayarwa da maniyyata aikin Hajji su 609 miliyan N752

Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta mayar da sama da Naira miliyan 752 ga maniyyata 609 da suka yi ajiya don aikin Hajjin 2020/2021.

Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Muhammad Sani Alhassan ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin Jigawa a ranar Asabar.

Ya ce Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta umarci hukumar da ta gaggauta mayar da kudin aikin Hajjin bayan hukumomin Saudi Arabiya sun sanar da hana aikin hajji zuwa wasu kasashe a wani mataki na dakile yaduwar cutar ta COVID-19.

Alhassan ya yi bayanin cewa maniyyata 1,165 suke aje kudin don aikin Hajji a 2020/2021.

“Daga cikin mahajjata 1,165, 609 an mayar ma su yayin da 556 ba su karbi kudin aikin Hajjin su ba,” in ji shi.

Ya ce ragowar maniyyata 556, wadanda ba su karbi kudin hajjinsu ba, za a yi la’akari da su a aikin na shekara mai zuwa.

Alhassan ya bukaci mutane da su ci gaba da yin addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali da kawo karshen cutar ta COVID-19 a duniya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *