fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Hadarin mota ya kashe mutane 11 a Kwara

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Kwara ta ce mutane goma sha daya ne suka mutu a ranar Asabar a wani hatsarin a wajen garin Ilorin.

Jonathan Owoade, kwamandan sashin, ya fadawa NAN a Ilorin cewa hatsarin ya afku ne kusa da “Mahadar Shao” sakamakon tsananin gudu.
Ya ce, “Hukumar FRSC ta samu kira da misalin karfe 6.35 na safe game da hatsarin da ya shafi motoci 2, motar bas ta kasuwanci da kuma wata motar da aka bayyana da safiyar yau kuma ta gano cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu.”
Owoade ya bayyana cewa cikin mutane ashirin da hatsarin ya rutsa da su, mutane goma sha daya suka rasa rayukansu yayin da wasu suka samu raunuka.
“An dauki gawawwaki goma sha daya zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin, yayin da wadanda suka samu raunuka aka kaisu wani asibiti da ke kusa da su domin yi musu magani.
Owoade ya gargadi masu ababen hawa game da karya dokokin kiyaye hanya da sauran masu amfani da hanya, musamman matafiya, da su yi wa direbobin motocin kasuwanci gargadi game da wuce gona da iri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *