Akalla mutane biyu ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a ranar Lahadin data gabata a kan hanyar Ado Ekiti-Iworoko dake jihar Ekiti.
Wasu Shaidun gani da ido sun shaida mana cewa a kalla mutane 12 ne suka samu raunuka daban-daban a mummunan hatsarin, wanda ya faru a daura da Jami’ar Jihar.
Sai dai anyi Nasarar kwashe wadanda suka samu raunuka inda aka kai su zuwa Asbiti.
Rahotanni sun nuni da cewa hadarin ya faru ne a sakamakon rashin kyan hanyar.