fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Hadarin Mota yayi sanadin mutuwar mutum 1 tare da jikkata wasu a jihar Bauchi

Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Bauchi wanda ya hada da motocin kasuwanci guda uku ya lakume rayukan mutum daya yayin da wasu da dama suka jikkata.

Hatsarin ya afku ne da misalin karfe 1 A ranar Litinin a Kauyen Dungal, mai nisan kilomita 10 daga garin Bauchi.

Wani Shaidar gani da ido mai suna Malam Umaru ya shaida wa manema labarai yadda lamarin ya faru inda ya bayyana cewa wani mai babur ne ya hadda sa faruwar lamarin a yayin da ya zo tsallaka titi.

A cewarsa, A yayin da mai baburin ke kokarin tsallake titi sai baburin ya mutum hakan ne ya sanya shi jefar dashi a tsakiyar titi wanda hakan ya hadda faruwar lamarin.

Bayan faruwar hatsarin ne dai Jami’a daga hukumar kiyaye hadura suka isa wajan da lamarin ya faru inda su kai Nasarar Ebe wadanda abun ya rutsa dasu zuwa Asbitin Tabawa belewa dake a jihar.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *