fbpx
Friday, May 14
Shadow

Hankalin ‘yan IPOB ya tashi sosai da kashe babban Kwamandansu, Ikonso, Ji abubuwan da suke cewa

A jiya ne dai Rahotanni suka tabbata cewa Sojojin Najeriya da gamayyar ‘yansanda da jami’an ‘yansandan farin kaya na DSS sun kai hari maboyar haramtacciyar kungiyar IPOB a jihar Imo.

 

Wannan samame yayi nasara sosai inda har ta kai ga an kashe mataimakin Shugaban kungiyar wanda kuma shine babban kwamandanta dake kula da hare-haren da ake kaiwa a yankin kudu maso gabas me suna Ikonso.

 

Kashe wannan gawurtaccen dan ta’adda ya tayarwa da kungiyar IPOB hankali wanda cikin gaggawa ta fitar da sanarwar cewa ain ya mata zafi kuma zata dauki fansa.

 

A sanarwar da kakakin kungiyar, Emma Powerful ya fitar jiya, yace zasu dauki fansa akan Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma wanda suka ce shine ya hada kai da jami’an tsaro aka kashe Ikonso. Kungiyar ta yi zargin cewa, Gwamna Hope Uzodinma ya nemi Ikonso ya zama Shugaban jami’an tsaron Egbube amma yakiya shine yasa aka kasheshi.

 

Da yawa ‘yan IPOB sun hau Shafukan sada zumunta suna nuna alhininsu akan mutuwar Ikonso wanda suka rika bayyanashi da wani gwarzo da ya sadaukar da rayuwarsa wajan yaki dan tabbatuwar kasar Biafra.

 

 

 

https://twitter.com/EdehAlexi/status/1386074975849918466?s=19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *