fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Har yanzu Muna Kewarka: Shugaban Real Madrid a sakon taya Ronaldo murnanar cika shekaru 35

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez ya taya Cristiano Ronaldo murnar zagayowar ranar haihuwar shi.

Shugaban Real Madrid ya yabawa dan wasan na Juventus a yayin da yake bikin ranar zagayowar ranar haihuwar shi karo na 35.
“Jinjina ga zakaran yan wasan kwallon kafa na duniya,muna kewar ka sosai”.
Cristiano Ronaldo  ya cika shekaru 35 ranar laraba, daga cikin sakonnin murna marassa adadi da duniyar kwallon kafa ta turo mai wannan sakone daya fito daga wurin shugaban Real Madrid Florentino Perez:
“Jinjina ga zakaran yan wasan kwallon kafa  na duniya,muna kawar ka sosai”.
Perez ya turo sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar dan wasan da yakai tsawon shekaru tara yana wasa a Real Madrid ne ta jaridar kasar Portugal wato Record.
Kuma jaridar ta kara da cewa akwai wani sako daya fito daga hannun dan wasan Atletico Madrid wato Joao Felix,Cewa ba shakka Ronaldo “shine zakaran yan wasan kwallon kafa na duniya” kuma yana da burin “cigaba da yin wasa”da shi da kuma kasar shi baki daya.
Ronaldo har yanzu zakarane a fagen jefa kwallo cikin raga. 
Ronaldo har yanzu babu wani abu da yake nuni akan gazawarsa akan aikin shi duk da yawan shekarun sa,Don yana da kwallaye 22 yanzu haka kakar bana,19 a Seria A, 2 a champions League,sai daya a gasar kofin italiya.
Gaba daya dai Ronaldo yaci kwallaye 722 a wasannin daya buga muhimmai:5 a sporting Lisbon,118 a Manchester United,450 a Real Madrid,50 a Juventus sai 99 da ya ciwa kasar shi.
Ronaldo na sa tsammanin cika kwallaye 100 wa kasar shi a wani wasan sada zumunci da zasu buga da Spain da Portugal ranar biyar ga watan yuni a filin Wasan na Metropolitano dake Madrid.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *